An Katse Taron Hafsan Sojin Najeriya Bayan Da COVID-19 Ta Kashe Wani Janar

Sojojin Najeriya yayin bikin samun 'yancin kai a ranar 1, 2018. (AP Photo/Olamikan Gbemiga)

A Najeriya, cutar COVID-19 ta halaka wani babban Janar din sojin kasar bayan da ya kamu da cutar wacce ake ganin farfadowarta a wasu sassan Najeriyar.

Rundunar sojin Najeriyar ta katse taronta na babban hafsa wanda ya hada hancin baki dayan manyan kwamandojin sojojin kasar a Abuja, inda ake tilawar irin nasarori ko akasi da rundunar ta samu da kuma tsara a shiryawa gaba.

Kakakin Rundunar Sojin Janar Sagir Musa ya fada cikin wata sanarwada ya aikewa Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa an dage taron.

An dakatar da taron ne nan take biyo bayan mutuwar wani babban Janar a daidai lokacin da yake halartar taron a Abuja.

An kuma umarci dukkan mahalarta taron da su yi gwaji sannan su kebe kansu.

Daukan matakin a cewar sanarwar ta biyo bayan sake ci gaba da yaduwar cutar numfashi ta COVID19 a Abuja babban birnin Najeriya inda ake taron.

Ko da yake, sanarwa ba ta ambci sunan janar din da ya rasu ba amma wasu majiyoyin sun bayyana cewa Manjo Janar O. Irefin ne.