Ma’aikatar tsaron Amurka ta fitar da sunayen wasu sojoji biyu da aka kashe a wani harin harbi da ya auku da safiyar jiya Lahadi a gundumar Sherzad da ke gabashin lardin Nangarhar na Afghanistan.
Sojojin sun hada da Sgt. Javier Jaguar Gutierrez, mai shekara 28, da Sgt. Antonio Rey Rodriguez shi ma mai shekara 28.
Wasu ma’aikatan soji guda shida kuma sun jikkata a lokacin da wani sojan kawance na Afghanistan ya bude wuta akan dakarun Amurka da na Afghanistan da bindigar da ake kira "Machine Gun" da turanci, a cewar mai magana da yawun rundunar Amurka a kasar.
Shah Mahmood, wanda shi ne gwamnan Lardin na Nangarhar, ya ce har yanzu dai ba a san ko sojan shigar burtu ya yi ba ko kuma lamarin ya faru ne bisa kuskure, ana dai ci gaba da gudanar da bincike.”
Wani jami’in ma’aikatar tsaron Afghanistan da aka sakaya sunansa saboda ba a ba shi izinin ya yi magana da kafafen yada labarai ba, ya ce maharin sojan Afghanistan ne ya kuma yi gardama da sojojin Amurka kafin ya bude masu wuta, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Associated Press ya ruwaito. Jami’in ya kuma ce, sojan ba shi da wata alaka da Taliban.