An kashe tsohon shugaban kasar Libya Moammar Gadhafi.
Dakarun gwamnatin majalisar wucin gadi sun kashe Gadhafi ne a hari na karshe da suka kai a garin haihuwarshi Sirte, watanni bakwai bayanda aka kaddamar da zanga zangar kin jinin mulkin kama karya da ya yi a kasar na tsawon sama da shekaru arba’in.
Shugaban Majalisar Wucin Gadi Mustafa Abdel Jalil ya tabbatar da mutuwar Gadhafi a wani taron manema labarai da ya kira a Tripoli. Gadhafi ya mutu yana da shekaru 69 a duniya. Amurka tace ta sami tabbacin mutuwar tsohon shugaban kasar daga jami’an kasar Libya.
Hotunan bidiyo da aka yayata a tashoshin talabijin na kasashen duniya sun nuna gawar Gadhafi jina-jina kwance a kasa, dakarun Majalisar Wucin Gadi sun kewaye shi wadanda daga baya suka dauki gawarshi zuwa Misrata.
Babu cikakken bayani kan yanayin da aka kashe shi. Mayakan Majalisar Wucin Gadi sun ce an sami Gadhafi yana boye a karkashin kasa, inda aka harbe shi aka kashe shi, yayinda mayakan suka murkushe sauran magoya bayanshi dake nuna tankiya a Sirte. Kungiyar tsaro ta NATO tace jiragen samanta na yaki sun kaiwa wadansu motocin dakarun dake goyon bayan Gadhafi biyu hari yayinda suke kuk-kurdawa a cikin Sirte jiya Alhamis.
Rahotanni daga Sirte na nuni da cewa, mayakan Majalisar Wucin gadin sun kuma kama dan Gadhafi Mutassim, sai dai akwai sabanin rahotanni kan ko yana da rai ko kuwa babu. Babu tabbacin inda danshi Saif al-Islam yake. Jami’an kasar Libya suna kyautata zaton cewa, ya gudu cikin hamadar kasar Libya.
Mayakan Majalisar Wucin Gadin sun yi bukin faduwar Sirte tare da harbe harbe a iska da kuma kada sabuwar tutar kasar Libya a inda a da ya kasance wuri na karshe dake karkashin ikon magoya bayan Gadhafi. Dakarun gwamnatin rikon kwarya sun mamaye garin Sirte na tsawon makonni, amma suka fuskanci tankiyar gaske daga magoya bayan Gadhafi wadanda suke da manyan makamai.
Jami’an Majalisar Wucin Gadi sun ce zasu ayyana ‘yancin kasar baki daya daga mulkin Gadhafi bayan kwace ikon garin Sirte gaba daya.