An Kashe Sojojin Isra’ila Takwas A Lebanon

Dakarun Isra'ila

Cikin daren Laraba, dakarun Isra’ilan sun kai wasu sabbin hare-haren sama a wata tungar mayakan Hezbollah da ke wajen kudancin birnin Beirut.

Isra’ila ta sanar a ranar Laraba cewa an kashe mata sojoji takwas a wani fada da dakarunta suka yi da mayakan Hezbollah a kudancin Lebanon.

Lamarin na faruwa ne kwana guda bayan da ta kadadamar da abin da ta kira “takaitaccen samamen kasa” da ta kai don lalata kayayyakin mayakan na Hezbollah.

Firaiminista Benjamin Netanyahu ya ce Isra’ilar ta shiga zazzafan yaki da Iran da kawayenta da suka kudiri aniyyar ganin bayanta.

Cikin daren Laraba, dakarun Isra’ilan sun kai wasu sabbin hare-haren sama a wata tungar mayakan Hezbollah da ke wajen kudancin birnin Beirut.

“Lokaci ya yi da za a dakatar da wannan yaki mara kan-gado da ke yaduwa, domin yana jefa mazauna yankin Gabas Ta Tsakiya cikin mummunan yanayi.” In ji Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.

A ranar Talata, ma’aikatar lafiya a Lebanon ta ce akalla mutum 55 suka mutu sannan 156 sun jikkata a hare-haren da Isra’ila ta kai cikin sa’o’i 24 da suka gabata tana mai cewa Isra’ilar ba ta banbance mayakan na Hezbollah da fararen hula a hare-haren da take kai wa.