An Kashe Mutane 25 A Gwabzawa Tsakanin Sojoji Da 'Yan Daba A Mexico

Hukumomi sun ce an gwabza wannan fada lokacin da sonjojin suke sintiri a wani gari dake yankin arewa maso gabashin kasar jiya alhamis.

Hukumomin kasar Mexico sun ce an kashe mutane 25 a wani fadan da aka gwabza a tsakanin sojoji da wasu mutanen da ake kyautata zaton 'yan daba ne a yankin arewa maso gabashin kasar.

Jami'ai suka ce an yi wannan gwabzawa jiya alhamis a lokacin da sojojin suke yin sintiri a garin General Trevino a Jihar Nuevo Leon, inda aka samu karuwar tashe-tashen hankula masu nasaba da fataucin muggan kwayoyi.

Jihar Nuevo Leon tana iyaka da Jihar Tamaulipas, inda wata kungiyar 'yan daba ta masu fataucin muggan kwayoyi ta kashe wasu baki 'yan kasashen waje su 72 a watan da ya shige.

Daya daga cikin mutane biyun da suka tsira da rayukansu a wannan kisan gilla a Jihar tamaulipas ya yi hira da gidajen telebijin jiya alhamis, inda yayi kira ga baki 'yan kasashen waje masu bi ta kasar Mexico a kan hanyarsu ta zuwa Amurka da su yi nesa da kasar Mexico.

Luis Freddy Lala Pomavilla, dan asalin kasar Ecuador, yayi wannan gargadin a lokacin da yake bayyana yadda 'yan bindiga suka sace su, suka dauke su zuwa wani gida inda aka daure musu hannuwa kafin a harbe su.

Lala, wanda ya ji ciwo a wuya lokacin wannan farmaki da aka kai musu, yace 'yan bindigar sun bayyana kansu a zaman 'ya'yan wata kungiyar 'yan daba ta masu fataucin muggan kwayoyi a Mexico da ake kira Zetas.

An kashe mutane fiye da dubu 28 a kasar Mexico tun lokacin da shugaba Felipe Calderon ya hau mulki a 2006, ya kuma kaddamar da yaki a kan gungu-gungun fataken muggan kwayoyi.