Shugaban wata ‘yar karamar coci ta Kirista a nan Amurka yace yana sake tunani game da shawarar da ya yanke ta janye shirin kona al-Qur’ani Mai Tsarki gobe asabar, a bayan da a bisa dukkan alamu tattaunawar da yake yi da shugabannin Musulmi a yankin ta wargaje.
Tun da farko, Reverend Terry Jones ya fada jiya alhamis cewa ya soke shirin kona Littafin na Musulmi a saboda ya cimma yarjejeniya da shugabannin Musulmi cewa zasu janye Cibiyar Al’adu da Masallacin da suek shirin ginawa a kusa da inda aka kai farmakin ta’addanci kan Amurka a birnin New York, su maida wani wuri dabam.
Amma kuma, limamin dake kula da shirin gina masallacin ya ce babu wata yarjejeniya makamanciyar wannan da aka cimma, har ma ya ce yayai mamakin jin wannan sanarwa da Reverend Jones ya bayar.
Daga bisani, reverend din yace wani malamin addinin Musulunci dake kokarin warware rikicin, Imam Muhammad Musri, yayi masa karya. Jones yace a yanzu yana sake tunani kan yin watsi da shirinsa, yana mai fadin cewa ba wai ya soke ba ne, ya dakatar ne kawai.
Imam Musri ya musanta abinda Paston yake fada, yana mai fadin cewa shi dai yana kokari ne ya shirya ganawa a tsakanin shi kansa da Jones da kuma Limamin na New York, Faisal Abdul Rauf domin tattaunawa kan ginin Masallacin. Musri ya fada ta cikin gidan telebijin na CNN cewa har yanzu ba a ma tabbatar da za a yi wannan ganawar ba.
Shugabannin addinai dabam-dabam a ciki da wajen Amurka sun fito da kakkausar harshe su na yin Allah wadarai da shirin Terry Jones na kona Al-Qur’ani gobe asabar.