An kasa cimma maslaha tsakanin kungiyoyi da Shugabanin Nijeriya

  • Ibrahim Garba

Masu zanga-zangar janye tallafin man fetur a Nijeriya

An tashi baram-baram a tattaunawar daren jiya Lahadi tsakanin Shugaban Nijeriya

An tashi baram-baram a tattaunawar daren jiya Lahadi tsakanin Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan da shugabannin kungiyar kwadago don kawo karshen zanga-zangar da aka yi sati guda ana yi don nuna rashin amincewa da tsananin tsadar farashin man fetur.

Shugabannin kungiyar kwadago sun ce za a cigaba da zanga-zangar. To amman sun saurari rokon shugaban kasar na dakatar da irin gangamin bisa kan titunan nan da ya tsananta a makon jiya. Shugabannin kungiyoyin kwadagon sun ce Shugaba Goodluck Jonathan ya ce masu akwai rahotannin da ke nuna cewa wasu masu wata manufa ta dabam na shirin fakewa da zanga-zangar. Don haka shugabannin kungiyoyin kwadagon sun ce ba su son su jefa rayuwar jama’a cikin hadari.

‘Yan Nijeriya dai na bakin cikin janye tallafin da aka yi a ranar zagayowar sabuwar shekara – wanda wannan shi ne daya daga cikin ‘yan abubuwa kalilan da ‘yan Nijeriya ke amfana daga arzikin man fetur dinsu.

Janye talllafin ya sa farashin man fetur ya rabanya, ya kuma kawo tsadar kayan abinci da kudin zirga-zirga a mota.

Ma’aikatan gwamnati sun shiga yajin aiki tun makon jiya, to amman sun janye barazanarsu ta katse ayyukan samar da danyen mai.

Shugaba Goodluck Jonathan ya ce a halin da ake ciki Nijeriya ba za ta iya cigaba da samar da tallafin dala miliyan dubu dari takwas ($8 billion) ba. Ya yi alkawarin yin amfani da kudin wurin samar da abubuwan more rayuwa.

Wasu kwararru sun ce tallafin barna ce kawai. To amman masu zanga-zangar sun ce almundahana ce ta jefa wannan kasa mai arzikin man fetur cikin talauci.