An Karrama Marigayi John McCain a Majlisar Tarayyar Amurka

  • Ibrahim Garba

Mahaifiyar marigayi John McCain ganga da akwatin gawarsa a ginin Majalisar Tarayyar Amurka.

Kamar yadda masu lura da al'amura da dama su ka yi hasashe tun farko, ana cigaba da jinjina da kuma karrama marigayi Sanata John McCain, wanda ya rasu kwanan nan sanadiyyar cutar kensa.

Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence na daga cikin dinbin Amurkawan da, a jiya Jumma’a, su ka karrama tare da yin bankwana ga marigayi Sanata John McCain. Mike Pence ya ce dadadden dan majalisar dattawan Amurkan, wanda kuma ya kasance jarumi wurin yaki, ya aiwatar da manyan ayyuka - har da ma wadanda su ka fi karfinsa.

Ya ce, “Shugaban kasa ya umurce ni in kasance a nan a madadin wannan kasar da ke yaba ma wannan gwani na ta, wanda ya bauta ma kasarmu a tsawon rayuwarsa a matsayin soja da kuma farar hula.” Pence ya fadi hakan ne a wurin hidimar da aka yi jiya Jumma’a a ginin Majalisar tarayyar Amurka.

Daruruwan ‘yan majalisa da ma’aikatansu ne su ka halarci hidimar, wacce Amurkawa 30 ne kadai aka taba yi masu irinta a tarihin kasar. An dora akwatin gawar McCain akan wata marika, wadda ake kira catafalque (katafalk) wadda aka yi amfani da ita a karon farko a 1864, lokacin da aka dora akwatin gawar Shugaba Abraham Lincoln a kanta.

Ba a gayyaci Shugaba Donald Trump wurin hidimar ta jiya Jumma’a ba, da kuma duk wani abin da ya shafi jana’isar McCain, wadda za a yi gobe Lahadi, saboda mummunar tankiyar da ta kasance tsaninsa da mamacin.

Mahaifiyar McCain, wadda ta yi shekaru 106 a duniya, da matsarsa da kuma ‘ya’yansa 7 sun kasance a wurin hidimar ta jiya Jumma’a.