Duk da ma labarin kama Yunusa wanda yake tsohon dalibi ne a jami’ar Kimiyya ta Minna ya faru ne tun tsakiyar watan jiya, yazo kuma dai dai da daukar karin matakan tsaro ga fadar shugaban Najeriya.
Takarda daga babban jami’in tsaron shugaban kasa Bashir Abubakar, ta umarci duk wani mai hulda da fadar ya tsaya a binciki motarsa yadda ya dace, da kaucewa al’adar wasu da kan wuce don su jami’an fadar ce ko kuma suna tuka wasu manyan mutane ne, don haka yazama wajibi daga yanzu duk wata mota mai duhun gilashi dole ne abude ta don ganin wanda ke ciki, a cewar sanarwar a irin wadannan motoci ‘yan ta’adda ke amfani wajen kai hari.
Kama Abdussalam Yunusa a Kano da labarin yace har ma ya fara tura wasu yan Najeriya Libiya, don karin samun horan ta’addanci, hakan bai zama abin mamaki ba ga wasu masana harkar tsaro.
Face an kai wanda ake zargin kotu, zai yi wuya a yanzu akara samun haske kan wannan labari, a tsarin jami’an tsaro na ganin labarai na shafar ayyukan bincikensu ne.
Ga Karin Bayani.
Your browser doesn’t support HTML5