An Kammala Taron Kwana Biyu Akan 'Yan Gudun Hijira a Maiduguri

Farfasa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasa

Mataimakin shugaban kasa Farfasa Yemi Osinbajo shi ya bude taron kwana biyu akan 'yan gudun hijira da aka yi a Maiduguri

Jiya aka kammala taron kwana biyu da mataimmakin shugaban kasa Farfasa Osinbajo ya bude a Maiduguri kan 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya daidaita.

Taron ya tattauna alauran da suka shafi 'yan gudun hijira da kuma shirin sake gina masu muhallansu tare da sake gina garuruwansu da kuma samar masu da abun yi.

Taron ya hada da hukumomin gwamnatocin tarayya da na jihohi da kungiyoyi masu zaman kansu a Najeriya da ma wasu daga kasashen ketare.

Taron ya tabo batun bada tallafi ga 'yan gudun hijiran amma an kara da jawo hankalin masu bada tallafin da su karkata zuwa Maiduguri saboda nan ne aka fi samun 'yan gudun hijiran..

Alhaji Sani Zoro dan majalisar tarayyar Najeriya kuma shugaban kwamitin tallafawa 'yan gudun hijira yace manufar taron shi ne yadda za'a taimakawa 'yan gudun hijiran su koma rayuwa irin wadda ta dace.

Yace sun sami tsarin da zai hada kan duk wadanda suke aikin tallafawa 'yan gudun hijira. An samu daidaito akan tsari daya yadda duk kungiyoyin zasu san aikin da kowa yake yi..

Akwai kuma tanadin hanyar da zasu dinga yada labaru ga duk 'yan gudun hijiran cikin gida da waje saboda jama'ar duniya ta san abun da ake ciki.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kammala Taron Kwana Biyu Akan 'Yan Gudun Hijra a Maiduguri - 4' 41"