KANO: An Kammala Taron Koli Kan Harkokin Tsaro

Shaidu a gidan dake Kano sun ce jami'an tsaro sun kashe wani mutum da mace mai ciki lokacin da suke farautar membobin kungiyar Boko Haram.

taron sha’anin tsaro a cikin al’uma da shiyya ta daya ta rundunar ‘yan sandan najeriya ta shirya a Kano ya yi kira ga gwamnati ta dauki matakan gaggawa wajen kirkiro guraben ayyuka ga ‘yan kasa, domin maganin shiga ayyukan tarzoma.

Taron wanda aka gudanar karkashin jagorancin tsohon sifeta janar na ‘yan sanda Ibrahim Kumassi, ya sami mahalarta daga jihohin Kano, Jigawa da kuma Katsina, wadanda suka hada da manyan jami’an ‘yan sanda, sarakunan gargajiya da kuma shugabannin al’umma, da lauyoyi da kuma kwararru kan zamantakewar al’umma.

Mashahuran malamai daga jami’oi daga cibiyoyin bincike dabam dabam na kasar suka gabatar da makaloli a kan fannoni da dama masu nasaba da tsaron kasa, wadanda suka hada da alakar kafofin watsa labarai da batun tsaro.Har ila yau, makalolin sun tabo tasirin tarzomar Boko Haram da tsagerun Naija Delta ga tsaron kasa.

A jawabin bayan taron da aka rubuta, an yi la’akari da cewa, akwai muhimmiyar rawa da aikin jarida zai taka ga tsaron kasa, an bayyana bukatar ‘yan sanda da manema labarai su yi aiki tare domin cimma manufa daya a fannin tsaron kasa.

An yi itifakin cewa, kafin ‘yan ta’adda su kai hari sukan zauna suyi nazari sosai, suyi la’akari da lokacin da ake taruwa, ta ina zasu shiga, ta ina zasu fita idan suka kai hari da dai bayanai makamantan haka. Saboda haka tilas ne gwamnati ta tashi tsaye sosai taga cewa tana da ma’aikata masu kwarewa da zasu yi aiki da kwakwalwa sama da abinda ‘yan ta’adda suke yi.

Daga Kano ga rahotan Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko.

Your browser doesn’t support HTML5

KANO: Taron Harkokin tsaro-3:22"