Taron ya jingine batun sabon kundun tsari inda ya mayar da abubuwan da aka tsara a matsayin shawarwari lamarin da ya sa ba'a yiwa majalisar kasar shiga sharo ba shanu ba.
Wata wakiliya a taron dake matukar marawa sabon kundun tsarin mulki baya tace illar tsarin mulkin yanzu shi ne cewa sojoji ne suka tsarashi. Matukar ba'a amince da sabon tsari ba tamkar wakilan sun bata lokaci ne, sun yi zaman banza na wata hudu.
Sanata Sa'idu Umar Kumo daya daga cikin wakilan taron kuma cikin wakilan gwamnatin Jonathan yace akwai wani kundun tsarin mulki da aka rubuta aka basu amma ba'a ambatoshi ba. Sabili da haka babu ruwansu dashi. Abun da suka sani su ne shawarwarin da suka bayar.
Bisa ga alamu babu wani bangaren da ya samu biyan bukatar duk abun da ya nema. Sai dai sun cimma matsaya domin gudun tada rigima. Dr Junaidu Muhammad yana ganin mai da zuciya nesa ne ya sa aka rufe taron ba tare da mari bare tsinka jaka ba.
Taron zai mikawa shugaba Jonathan kundaye ukun ranar Alhamis mai zuwa daga bisani ya turawa majalisa.
To sai dai 'yan majalisar sun ce su ba zasu karbi kundayen ba.
Ga rahoton .
Nasiru Adamu El-Hikaya
Your browser doesn’t support HTML5