Yau wakilan zasu zauna akan batun sabon kunidin tsarin mulki da aka ruwaito wai taron ya tsara.
Kudurorin sabon tsarin mulkin wai sun shafi wa'adin gwamnoni ne da shugaban kasa da kafa 'yansandan jiha da soke ko rage kananan hukumomi.
Wakilin taron Janaral Dan Ali yace sam ba zasu amince da sabon kundin tsarin mulki ba. Yace sai dai idan nasu ne can, wato na 'yan kudanci domin 'yan majalisu suna da kundun tsarin mulki. Kundun tsarin mulki ba haka kawai yakamata ya zo daga sama ba sai dai idan za'a samu kundun tsari biyu.
Akan kundaye kusan shafi dubu uku da aka basu su karanta Janaral Dan Ali yace babu wanda zai iya karance kundayen cikin kwana biyu. Sun yi korafin a basu sati daya domin su samu lokacin karantasu amma aka ki. Amma ya ba wakilan shawara. Yace kowa ya duba shafin da yake da alaka da kwamiti dinsa. Ya duba ko akwai kari ko kuma akwai wasu abubuwa da aka cire domin su sani. Yace ko menene suka shirya yi ta bayan fagge zasu wargazashi.
Amma wakili daga arewa maso gabas Isa Tafida yace ba'a fahimci lamarin ba ne shi ya jawo tsegumin da ake yi. Yace abun dake cikin kundun shawara ce. Idan majalisun tarayya sun amince na jihohi kuma sun amince ai magana ta kare. Yace wadan dake shugabancin kwamitoci su ne suka ci da zuci suka nuna kamar wani sabon kundun tsari ne. Sasu san dalili ba. Ba wai an canza kundun tsarin mulki ba ne. An cigaba da gyara ne.
Akan watakila suna kokarin su sa batun wa'adin shugaban kasa da na gwamnoni cikin tsarin ne sai Tafida yace dama abu ne da ya zo amma baya cikin sabon kundun tsarin. Duk abubuwan da aka sa cikin kundun abubuwan da suka yadda ne a kai. Walau gaba dayansu sun yadda ko kuma kashi 75 cikin 100 sun yadda. Babu wani abu daya da suka jefa kuri'a a kai.
Wakilai daga Neja Delta na goyon bayan sauyin haka ma Yarbawa dake son a koma tsarin yankin larduna.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya