Wani jami'in hukumar alhazan Najeriya ya tabbatarwa wakilin Muryar Amurka cewa sun kwashe duk alhazan kasar da suka biya suka kuma samu biza sai dai 'yan kalilan da suka samu matsala saboda wasu dalilai
WASHINGTON, DC —
Akwai irin wadanda basu san fasfo dinsu sun kare ba sabili da haka ba'a basu biza ba. Wasu kuma fasfo dinsu zai kare kasa da wata shida sabanin abun da dokar kasa da kasa ta tanada na cewa duk fasfo da zai kare kasa da wata shida ba za'a buga biza akansa ba.
Bana Saudiya ta baiwa Najeriya kejerun alhazai 76,000. Duk wadanda suke da biza sun samu sun shiga kasa mai tsarki.
Za'a yi hawan Arafa ranar Juma'a sabili da haka sallah ta kama ranar Asabar ke nan. Cikin alhazan Najeriya sama da kashi saba'in sun kai ziyara zuwa Madina. Sauran bayan hawan Arafat zasu je suyi tasu ziyarar kafin su kama hanyar zuwa gida Najeriya.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5