Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu ba a Fara Jigilar Maniyatan Jihar Adamwa ba


Hajji
Hajji

An kusan kammala jigilar maniyatan jihar Taraba, amma an sami akasin haka a jihar Adamawa

An kwashe wasu Maniyatan jihar Taraba zuwa kasa mai tsarki, wasu kuma na harama a filin saukar jiragen sama na Yola. Kawo Yanzu, mutane kalilan ne suka rage basu tashi ba.

Alhaji Habibu Almaki, sakataren hukumar Alhazan jihar Taraba, yayi Karin haske akan nasarorin da suka samu a jigilar maniyatan jihar. Inda yace bisa ga tsari da yau an kammala kwashe maniyatan amma gobe in Allah Ya kaimu za a kammala.

Yayinda maniyatan na jihar Taraba ke ta farin ciki, su kuma takwarorinsu na jihar Adamawa wadanda kawo Yanzu ma ba a fara jigilarsu ba, na nuna takaicinsu akan tsaikon da suke zargin kamfanin jiragen Kabo ya janyo masu. Wani da akayi hira da shi ya fadi cewa da an kawo jirgin da mutane sun fara tashi amma ga dukan alamu jirgin ya fara jin jiki.

Wakilin muryar Amurka a Adamawa Ibrahim Abdul’aziz, yayi kokarin jin ta bakin jami’an kamfanin na Kabo amma abin yaci tura. Domin babban jami’in da aka turo don gudanar da aikin jigilar maniyatan Mr. Steve, bai ce uffan ba ga manema labarai.

Jami’an hukumar Alhazan jihar Adamawa sun gayyaci Mr. Steve inda ya bayyana masu cewa suna kan kokarin samo jirgin da zai kwashe maniyatan.

Haka kuma duk wani kokarin ji daga bakin babban jami’in hukumar Alhazan jihar, Alhaji Zakari Ya’u Al’umma ya faskara. Amma wata majiya ta fadi cewa babban jami’in na gudanar da wani taro da manyan jami’an hukumar Alhazan jihar Yanzu haka.

Ga Ibrahim Abdul’aziz da Karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:35 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG