An Kammala Atisayen Sojojin Ruwa Mafi Girma A Duniya.

Tambarin OBANGAME EXORESS

Atisayen wanda rundunar sojojin ruwan Amurka dake Afirka wato U.S.NAVAF ta jagoranta ya tattaro baki dayan manyan hafsoshin rundunonin aikin ruwa na kasashen duniya.

An gudanar da Babban taron manyan Haffoshin dakarun ruwa a matsayin wani bangare na wannan atisayen wanda ya maida hankali sosai kan tsaro a gabar takun Guenea.

Cikin jawabinsa, Babban Hafsan Hafsoshin Rundunar sojin ruwan Najeriya, Vice Admiral Ibas Ekwe Ebot ya ce Ana tafka miyagun laifuka na kasa da kasa a gabar takun Guenea kuma Masu ta'asar na kai komo ne daga kasa zuwa kasa tunda a takun ba wani takamman wurin da za a ce shine iyakar wannan kasa da waccan kasa.

Admiral Ibas ya kuma ce batun fashi a cikin teku shima wata kalubale ce ga sojojin ruwa na kasashen duniya, yaa kuma daya daga cikin dalilan da yasa aka krkiro sojin ruwa.

Wani Hafsa mai murabus a rundunar sojojin ruwa, M.I. Salman yace irin wannan atisayen abune da zai amfani duk masu ruwa da tsaki ganin muhimmancin gabar takun Guenea ga duka kasashen.

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina

Your browser doesn’t support HTML5

Atisayen mayakan ruwa-2:20"