An Kame Shugabannin Hamayyar Venezuela Biyu

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro

Amurka ta yi Allah wadai da matakan gwamnatin kama-karyar kasar Venezuela, bayan kame wasu shugabannin hamayyar kasar biyu.

Shugaban Amurka Donald Trump, yace yana ‘daura hakkin tabbatar da "lafiya da tsaron" shugabannin hamayya biyu da 'yan sanda suka kame cikin dare akan shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro.

A wata sanarwa da ya fitar a daren jiya Talata, Shugaban na Amurka yayi Allah wadai da matakan da gwamnatin kama-karya ta Maduro take dauka. Sanarwar ta ci gaba da cewa Lopez da Ledzema, fursinonin siyasa ne da gwamnatin kasar take tsare da su ba bisa ka'ida ba.

Fefan bidiyon da aka gani a dandalin Twitter, ya nuna jami'an tsaron Venezuela suna jan shugabannin hamayyar Leopoldo Lopez, da Antonio Ledezma daga gidajensu aka saka su cikin motoci.

Daman dai jagabannin adawar biyu dai na karkashin ‘daurin talala kan wasu laifuka da ake tuhumarsu.

Babbar kotun Venezuela ta ce wasu bayanan sirri sun nuna alamun cewa Lopez da Ledezma na shirin arcewa, su bar kasar. Haka kuma kotun tace sun saba yarjejeniyar ‘daurin talalar da ake musu ta hanyar yin kamfen din siyasa da kuma yin magana da kafafen yada labarai, inda suke ‘kara karfafa gwiwar al’umma da su yi wa gwamnatin Maduro zanga-zanga.