An Kame Ma’aikatan Gidan Yari Uku Kan laifin Kashe Fursuna

Corrections officers wave to passing motorists who cheered them after the second of two escaped prisoners was apprehended, June 28, 2015, in Constable, New York.

Jami’ain ‘yan sanda a jihar California sun kame wasu ma’aikatan tsaron gidan Yari su uku a dalilin samun gawar wani fursuna dauke da raunuka.

Mai magana da yawun ‘yan sanda garin Santa Clara, James Jensen yace sun kame ma’aikatan uku Rafael Rodriquez mai shekara 27 da Jereh Lubrin mai shekara 28 da Matthew Farris mai shekaru 27, da kuma tuhumar su da laifin kisa.

Mai binciken musabbabin mutuwa Dakta Joseph O’Hara yace fursunan mai suna Michael James Pipkin mai shekaru 31 ya mutu ne a dalilin duka da akayi masa, inda aka ji masa raunuka masu yawa.

Daya daga cikin jami’an ‘yan sandan dai ta barke da kuka alokacin da take baiwa iyalan mutumin hakuri kan abin da ya faru, ta kuma kira ma’aikatan gidan Yarin da suka aikata wannan ta’asa a matsayin mugaye, kuma za’a tabbatar anyi musu hukunci kamar kowa.