Shafin zumunta na facebook, shafi ne da idan akayi amfani da damar da yake badawa, zai amfani mutane da dama a rayuwar su. Wani shahararen marubuci mai suna Brad Meltzer, a shekarar 2013 ya wallafa wani littafi, wanda ya sadaukar da wanna littafin ga wata malamar da ta koyar dashi, Tarihi a lokacin da yake makarantar Firamari a shekarar 1987.
Ya samu labarin cewar wanna malamar tashi Ellen Sherman, mai shekaru saba’in da daya 71, tana fama da rashin lafiyar da take bukatar a dasa mata sabuwar Zuciya. Ya rubuta a shafin shi na facebook cewar, duk wanda zai iya taimaka ma wannan matar da Zuciyar shi daya, don ceto rayuwar ta, a na bukatar hakan cikin gaggawa.
A nashi tunanin wanna itace babbar rashin hankali da yataba yi a rayuwarshi, ya tambayi dinbin mutane da yake abokantaka da su ta shafin facebook, bayan bai taba haduwa da mafi yawancin su ba. Amma Ba’a ayi wata-wata ba sai ga sama da mutane dari 100, sun yadda zasu bada zuciyar su ga malamar shi.
Daya daga cikin su itace Amy Waggoner, daga jihar Vajiniya, wadda suka zamo abokai da marubucin a shafin shi na facebook, a shekarar da ta gabata. “Bayan ta aika da sakon cewar zata bada nata zuciyar ba’a amsa mata ba, sai ta sake aikwa da sakon a karo na biyu, kana tasamu amsa. An kuma gudanar da wanna chanjin zuciyar, a satin da yagaba ta, kuma likitoci sun tabbatar mata da cewar zata iya komawa aikinta, don kuwa lafiyar ta lau.
A nan za’a gacewar shafin facebook ya kubutar da wanna tsohuwa da ga sauran wahalhalu na duniya, sanadiyar wanna dalibin nata mai abokai da suka kai fiye da dubu sittin 60,000 a shafin shin a facebook.