Rundunar sojan Najeriya na Operation Lafiya Dole dake garin Maiduguri, ta baiyana korar wasu jam'ian sojan ta uku da aka kama, ake kuma zargin cewa sun kasance cikin 'yan kungiyar asiri, kuma masu garkuwa da mutane.
An dai kama sojojin ne cikin wasu mutane 25 da maharba suka kame a wani Otal da ake kira Bagani a filin Maidaribe, dake baya-bayan gari a daren Asabar.
Kamun ya hada da wasu daliban Makarantar Jami'an Maiduguri guda 10, dana makarantar Ramat su 2, wadanda baki dayansu ake zargin 'ya 'yan kungiyar Asiri, kuma masu 'yunkurin karkuwa da mutane ne.
Cikin kayan da aka kama dai sun hada da kwarya da layu da wasu bakaken kaya, dama wani abin da ake zargan cewa jinine a wasu jarkoki.
Majo Janal Olushegun Adeneye wanda shi ne kwamandan rundunar sojan na Operation Lafiya Dole dake garin Maidugrin, yayi bayani kan wadannan kaya.
Shima kwamishinan 'yan sandan jihar Borno, Mohammed Ndasu Aliyu ya yi bayani ga manema labarai game da wadannan mutane da aka kama.
Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5