An kama mutanen ne akan hanyarsu ta zuwa Mashekari cikin jihar Taraba.
Kakakin rundunar 'yansandan jihar Adamawa DSP Usman Abubakar ya tabbatar da kama mutanen kuma yace ana tsare dasu. Rundunar ta gargadi makiyaya da manoma da su gujewa daukar doka a hannunsu. Ban da haka masu ruwa da tsaki a karamar hukumar sun yi amanna zasu zauna su kawo zaman lafiya tsakaninsu.
'Yansandan sun cigaba da bincike kuma nan ba da dadewa ba zasu gurfanar dasu a gaban kuliya. Ya gargadi jama'a cewa idan akwai abun da basu yadda dashi ba su gayawa mahukunta su ne zasu dauki matakin da ya dace.
Su makiyayan suna kan hanyarsu ne ta zuwa Mashekari cikin jihar Taraba lokain da hatsaniyar ta faru a yankin Bali dake cikin karamar hukumar Dosa..
Mai magana da yawun Fulanin yace suna kan hanyarsu ta zuwa Taraba ne sun kai Bali sai aka far masu aka kashe akalla Fulani 20 kana aka lalata dukiyoyi har ma shanu 300 sun bace ba'a san inda suke ba. Yace mutanen garin sun cigaba da kashe shanu. Yace babu abun da ya faru haka kawai aka far masu.
Lamarin ya auku gaf da lokacin da kwamishanan 'yansandan jihar yake kafa kwamitin sasanta al'ummar Yungur da wasu makiyaya a yankin. Alhaji Sanusi Bara jigo ne a kungiyar makiyaya ta Najeriya wato Miyetti Allah ya kuma yi karin haske. Ya kira gwamnati ta mayarda hankali akan rigngimun dake faruwa a yankin arewa. Yace yana gayawa Fulani su zama masu bin dokoki. To amma sarakunan gargajiya na kabilu da gangan suke haddasa tashin hankali tsakaninsu da Fulani.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5