An Kama Wani Mutun Dauke Da Bindiga Kusa Da Gangamin Yakin Neman Zaben Trump A California

DOnald Trump

Hukumar ‘yan sandan farin kaya ta Amurka tace tana sane da kamen kuma babu ko guda daga cikin Trump ko mahalarta gangamin daya shiga wani hatsari a lamarin, daya afku a ranar Asabar.

Jami’an tsaron dake baiwa Donald Trump kariya yayin gangamin yakin neman zabensa a yankin Coachella na jihar California, sun bayyana cewa sun kama wani mutum dauke da kananan bindigogi 2 ba bisa ka’ida ba, daya cike da harsashai, a cewar sanarwar da ofishin ‘yan sanda na yankin Riverside a jiya Lahadi.

Hukumar ‘yan sandan farin kaya ta Amurka tace tana sane da kamen kuma babu ko guda daga cikin Trump ko mahalarta gangamin daya shiga wani hatsari a lamarin, daya afku a ranar Asabar.

“Duk da cewa ba’a kama kowa ba a matakin tarayya, har yanzu ana cigaba da bincike,” a cewar hukumar dake da alhakin bada kariya ga shugabanin kasa da ‘yan takarar shugaban kasa a sanarwar da ta fitar da hadin gwiwar hukumar FBI mai binciken manyan laifuffuka a Amurka da ofishin antoni janar din kasar.

A cewar tawagar ‘yan sandan shiya, an saki mutumin mai shekaru 49 da haihuwa mai suna Vem Miller daya fito daga Las Vegas a kan beli, kuma zai fuskanci tuhuma a gaban kotu a ranar 2 ga watan Janairu mai zuwa.

Al’amarin na zuwa bayan yunkurin hallaka Trump sau 2 a baya-baya a Pennsylvania inda harsashe ya gogi kunnensa, sai kuma na 2 wanda bai yi nasara ba, a filin wasan golf na jihar Florida.