Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta da ke aikin “Operation Whirl Punch” karkashin runduna ta daya, sun cafke wani shahararren mai samar da makamai ga ‘yan bindigar jihar Zamfara.
A cikin sanarwar da mukaddashin daraktan labaran rundunar, Kanar Muhammad Dole, ya aika wa sashin Hausa na Muryar Amurka, ta ce sojojin sun cafke Rabilu Akilu a shingen binciken ababan hawa a Borgu dake karamar hukumar New Busssa cikin jihar Niger.
An dai Sami bindigogi kirar gida guda 21, da wasu karin bindigogi kirar kasar Ghana guda 15 da Kuma wasu kananan bindigogi guda 10. Sannan da kuma gidan harsasai na bindigogin guda 343.
Wannan mai safarar makaman, Rabilu Akilu, wanda dan asalin jahar ta Zamfara ne daga kauyen Dangulbi a karamar hukumar Maru, wanda yanzu haka ya na hanun jami'an tsaro wadanda su ke gudanar da bincike, kamar dai yadda wakilinmu a Abuja Hassan Maina Kaina ya aiko ma na.