Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde ya ce hukumomin tsaro sun kama wadanda suka shirya kalankuwa a shiyar Bashorun na birnin Ibadan da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 35 kuma jihar za ta tabbatar sun fuskanci shari’a.
Gwamnan ya bayyana lamarin da ranar takaici ga gwamnatin jihar Oyo sannan ya jajantawa iyayen da suka rasa ‘ya’yansu.
An yi asarar rayuka da dama a turmutsutsin da ya faru yayin wani bikin kalankuwa a Ibadan, babban birnin jihar oyo.
Kakakin ‘yan sadan jihar Oyo SP Osefiso ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da aka rarrabawa manema labarai a Ibadan.
SP Osifeso ya tabbatar da mutuwar kananan yara maza da mata 35 a turmutsutsi a makarantar Islamiyya da ke shiyar Bashorun a Ibadan don karbar kyaututtukan kirsimeti daga tsohuwar mai ɗakin Sarki Ooni na Ife, Naomi Silekunola Ogunwusi da mai gidan rediyon Agidigbo FM, Oriyomi Hamzat waɗanda su ne ake yi wa kallon haddasa al'amarin.