Rundunar ‘yan sandan Jihar ta tabbatar da kama motar, inda kakakin rundunar D.S.P Lawan Abdullahi ya bayyana taka-mai-mai yadda lamarin ya faru.
“’Yan sandan mu wadanda suke kan sha-tale-tale, sune suka kama wata mota kirar ‘Golf’, motar nan akwai samfurin takardun zabe a ciki. An kuma kama matukin motar guda daya, to amma binciken mu ya nuna cewa wadannan takardu na zabe da aka samu, takardu ne na ilimantar da masu jefa kuri’a”, a cewar D.S.P Abdullahi.
Wannan yazo ne a lokacin da jama’a ke bude idanu da kunnuwa domin hana magudin zabe a babban zabe dake tafe a Najeriya. Wannan ba shine karo na farko da ake kama irin wannan mota ba, daga bisani a sake ta, ta kama gabanta.
A halin yanzu shugaban Najeriya Goodluck Jonathan na yakin neman wa'adi na biyu a mulkin Najeriya karkashin inuwar jam'iyyar PDP, sai dai tsohon shugaban Najeriya a zamanin mulkin soja, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya shine babban mai kalubalantar shi a karkashin jam'iyyar APC. Duk bangarorin sun dauki alwashin neman goyon bayan masoyansu domin tabbatar da zabe cikin kwanciyar hankali da walwala.