Sai dai duk da haka, wasu ‘yan Najeriya a Kano na kukan rashin samun katin.
Mallam Abdulkarin Muhammad cewa yayi “ban karbi katin zabe na ba, naje, naje, naje idan an dauko ana duddubawa, sai ace wai mu tamu, ta lambar akwatin mu, wai ta kone. Ance mu kara dawowa, naje, mun dawo, an dudduba, amma har yanzu hakon mai samu ruwa ba.”
Malama Maryam Umar ma tana da korafi “ban karba ba, munje bamu samu ma’akatan ba, kuma bamu samu katin zaben ba. Wani lokacin idan munje, masu bayarwa basu fito ba, wani lokacin idan munje bamu ga namu ba. Naje ya kai sau biyar, ko shida. Gaskiya yanzu na hakura, sai wata shekara.
Amma wasu dayawa kuma sun samu cikin sauki.
Kiddiga dai ta nuna cewa fiye da kaso 64 cikin 100 na mutanen da suka yi rijista a Kano, sun karbi nasu katunan zaben ya zuwa yanzu, wato fiye da mutum miliyan 3 kennan, daga cikin sama da mutum miliyan 4 da suka yi rijista.