An Kama Masu Garkuwa Da Mutane 33 a Jihar Zamfara

'Yan Sanda A Jihar Zamfara.

'Yan Sanda A Jihar Zamfara.

Jami’an tsaro sun yi nasarar cafke wasu masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa har 33 a jihar Zamfara.

Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle, shi ne ya bayyanawa manema labarai wannan nasara da jami’an tsaron suka samu.

Ya kuma bayyana cewa yawancin mutanen da aka kama ‘yan asalin garin Gusau ne.

A baya dai gwamnan ya bayyana cewa gwamnati na sane da dukkan wadanda ke da hannu a ayyukan satar mutane, inda ya ce aikin wadanda aka kaman shi ne da zarar an yi garkuwa da mutane, sune suke karbar kudade su kuma mika su ga ‘yan bindigar dake cikin dazuka.

Karin bayani akan: Aminu Waziri Tambuwal, Bello Muhammad Matawalle, jihar Zamfara, jihar Sokoto, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Cikin wadanda aka kaman akwai wani ma’aikacin kashe gobara a jjihar Zamfara, wanda hakan ya sa gwamnan yin kira ga al’ummar jihar da su rika saka ido tare da kare kansu ga irin wadannan munana aiyuka.

Daga makwabciyar jihar Sokoto, gwamna Aminu Waziri Tambuwal, ya kai ziyarar jajantawa mutanen Zamfara bisa asarar rayukan da aka samu, tare da bayyana yunkurin da gwamnonin shiyyar ke yi na ganin an kawo karshen rashin zaman lafiya da ya addabi mutane.

Domin karin bayani saurari rahotan Sani Shu'aibu Malumfashi.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kama Masu Garkuwa Da Mutane 33 a Jihar Zamfara - 3'14"