Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakon Buhari Ga ‘Yan bindiga: Kada Ku Yi Tsammanin Kun Fi Mu Karfi Ne 


Shugaba Buhari (Instagram/ muhammadubuhari)
Shugaba Buhari (Instagram/ muhammadubuhari)

'Ya kamata masu aikata wadannan manyan laifuka, su daina gani kamar gwamnmati ba ta da karfin da za ta murkushe su.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya gargadi ‘yan bindiga da ke kai hare-hare akan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci irin wannan ta’asa ba.

Buhari na magana ne cikin wata sanarawa da kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar inda yake jajintawa al’umar jihar Zamfara kan harin da ‘yan bindiga suka kai a wasu yankunan jihar.

Gomman mutane ne suka rasa rayukansu, bayan wasu hare-hare da ‘yan bindigar suka kai a ranar Laraba akan kauyukan jihar ta Zamfara.

Rahotannin sun ce sama da mutum 80 aka kashe a hare-haren wadanda suka hada da kananan yara, mata da dattawa.

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle
Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle

“Ya zama dole a dakata da irin wannan mummunan danyen aiki na rashin hankali da ake yi akan mutanen da ba su san hawa ba balle sauka.” Sanarwar ta ce.

“Ya kamata masu aikata wadannan manyan laifuka, su daina gani kamar gwamnmati ba ta da karfin da za ta murkushe su.”

Karin bayani akan: Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Garba Shehu ya ce, shugaba Muhammadu Buhari, ya ba jami’an tsaro umurnin su dauki matakan gaggawa wajen magance hare-haren ‘yan bindigar, yana mai cewa “wani shirin kai farmaki da aka kaddamar a yankin karamar hukumar Maru, zai kawo karshen maharan.”

Ya kara da cewa, gwamnatinsa ba za ta lamunci kai hari akan mutanen karkara, “wadanda suke fama da talauci da sauran matsalolin tattalin arziki.”

Sanarwar ta kuma ba al’umar jihar Zamfara tabbacin cewa, “duk da irin koma bayan da aka fuskanta a kokarin da ake yi na kare rayukan al’uma, ba za mu yi kasa a gwiwa ba a yunkurin da muke yi na ganin mun kawar da makiyan jama’a.”

XS
SM
MD
LG