A lokacin da aka gano bindigogin, a wani bangaren an gano galan-galan na man fetur da ake hasashen ana isar da su ne domin amfanin ‘yanta’adda.
Binciken da jami’an tsaron jandarma suka kaddamar a ranar Alhamis din da ta gabata sakamakon wasu bayanan da aka tsegunta ne ya baiwa wadanan askarawa damar gano kasuwar fataucin makamai dake ci ta bayan fage a kauyen Kaon a gundumar Tchintabaraden dake jihar Tahoua.
Kakakin hukumar Gendarmerie Nationale Commandant Yahaya Masallatci ya yi mana karin bayani.
A baya wadanan makamai asamamen da suka kai jami’antsaron jandarman jihar Tahoua sun kama tarin galan-galan na man fetur da ake kyautata zaton ana shirin isar da su ne zuwa yankunan dake fama da tashe tashen hankula domin amfanin ‘yan ta’adda.
Wannan al’amari na faruwa ne a wani lokacin da kusan akasarin hankulan jama’ar Nijar ya karkata akan ce-ce-ku-cen siyasa wanda ke zama wata damar da ke baiwa masu aikata myagun aiyukan sukuni suna cin karensu ba babbaka inji wani dan Siyasa Soumaila Amadou.
Shugabanin hukumar tsaro ta Gendarmerie Nationale sun bukaci jama’a akan maganar sanar da jami’an tsaro a duk lokacin da aka lura da wata bakuwar ijiya kokuma wasu abubuwan da ake shakku akansu ta hanyar kiran wayar taraho mai lamba 16 domin bada bayanai.
A saurari rahoton wakilin muryar Amurka a Yamai Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5