Jami’an tsaron farin kayan sun shafe makonni biyu suna fakon Dasukin, bayanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin kama wadanda ke da hannu kan kwangilolin sawo makamai na fiye da Naira biliyan dari shida da kuma sama da dala biliyan biyu.
Sauran wadanda kamun ya shafa sun hada da hafsoshin soja na da, da na yanzu, tsohon ministan tsaro Bello Halliru, tsohon gwamna Attahiru Bafarawa, Bashir Yuguda da kuma shugaban tashar talabijin ta AIT Raymond Dokpesi.
A cikin hirarsu da Muryar Amurka, Bashir Baba, wani mai sharhi kan lamura ya bayyana cewa, babu wani wanda yafi karfin gwamnati. Kasancewa ana batun canji, matakan da gwamnatin Buhari ta dauka manuniya ce cewa, zata ba marada kunya.
Masu kula da lamura suna bayyana cewa, kamata ya yi shugaban kasar ya dauki matakan gaggawa na tuhumar dukan wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa ba kamar yadda aka saba yi a lokutan baya inda ake shafe shekara da shekaru ana shari’a ba tare da hukumata wanda aka kama ba.
Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Nasiru Adamu Elhikaya ya aiko daga Abuja
Your browser doesn’t support HTML5