An Kaiwa Masu Zanga-zanga Hari a Sudan

Masu zanga-zanga a birnin Khartoum

‘Karan harbin bindiga ya barke da yammacin ranar Litnin a birnin Khartoum, a lokacin da jami’an tsaro suka yi arangama da masu zanga-zanga a daidai lokacin da kwamitin soji dake rike da mulki a Sudan ya sanar da cewa an cimma yajejeniya da shugabannin masu zanga-zangar akan mulkin kasar.

Jami’an tsaro sanye da kaki dauke da makamai sun rika kawar dae shingayen da masu zanga-zangar suka kakkafa, suna harbi da bindiga da amfani dabarkonon tsohuwa, da kuma dukan masu zanga-zangar. Wadansu shaidun gani da ido sunce an kashe mutane da dama an kuma raunata wasu.

Kwamitin Sojin dake mulki a Sudan ya zargi wadansu bata gari da bai bayyana ba, da harin da aka kai, ya kuma ce wani jami’ai Sojan dan sanda dake da matsayin Major na daga cikin wadanda suka mutu.

Amma babu masaniyar ko wanene yake da alhakn harbin da aka yi.

Yassir Mohamed wani lauya yayi Magana da Muryar Amurka bayan da ya tserewaharbin bindiga ya ce.

Ya ce abin mamaki shine ba zasu iya fadin wanda yakai musu hari ba. Amma, daga abin da ya gani da ya kuma fuskanta, da alamun wasu sojojin boye ne ko wasu masu shigar burtusuka haifar da wannan tashin hankali.

A halin da ake ciki kuma, sojoji akan wata babbar mota dake dauke da babbar bindiga mai sarrafa kanta suna zagayawa a kusa da masu zanga-zangar, lamarin dake da rikitarwa wajen sanin ko sune suka fara kai harin.