Shaidu sun ce wani harin da aka kai cikin wani babban dakin karatun Jami’ar Bayero ta Kano, wanda Kiristoci ke yin Ibada a ciki, ya halaka mutum 15 a kalla.
Haka kuma akwai labarin cewa dimbin mutane sun jin ciwo, amma ba a tabbatar da kamalallen adadin su ba.
Shaidu sun ce maharan sun je jami’ar ta Bayero ce a kan babur da kuma mota, su kai ta jefa boma-bomai tare da yin harbi.
Nan take babu wanda ya fito fili ya dauki alhakin kai harin, amma a can baya kungiyar Boko Haram ta masu tsattsauran ra'ayin addini ta sha kai hare-hare kan Kiristocin Najeriya.
Kirsimetin da ya gabata ma wasu fashe-fashen boma-bomai a wurare hudu daban-daban a kalla sun halaka mutane 39, da su ka hada da wasu masu dimbin yawa a Majami'ar Katolika da ke kusa da Abuja, kuma kungiyar Boko Haram mai haramta ilimin zamani salon na kasashen Turawa, ta dauki alhakin kai wadannan hare-hare.
Kungiyar ta ce so ta ke yi ta kafa wata kasar Islama a arewacin Najeriya kuma ta ce ba ruwan ta da gwamnatin kasar, sannan kuma ba ta bin kundin tsarin mulkin kasar.
Wasu daruruwan mutanen sun mutu a bara cikin hare-haren boma-bomai da harbe-harben da aka dorawa Boko Haram.