Sokoto, Nigeria - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ce ta kama matasan biyu ranar Alhamis 12 ga watan Mayu, a lokacin da dalibai suka kashe Deborah Samuel kuma suka kona ta akan zargin ta yi batanci ga fiyayyen halitta.
A wannan Litinin 16 ga Mayu ce aka gurfanar da matasan biyu: Bilyaminu Aliyu da Aminu Hukunci, wadanda dalibai ne a kwalejin ta koyar da malanta ta Shehu Shagari.
Sai dai bayan da aka karanta musu laifin da ake tuhumarsu wanda ya yi sanadin salwantar rayuwar Deborah sun ki aminta da laifin abinda ya sa dan sanda mai gabatar da kara, Inspector Khalil Musa, ya nemi kotun da ta kara basu lokaci domin fadadawa da kammala bincikensu.
Jagoran lauyoyi dake tsaya wa wadanda ake ake tuhuma Farfesa Mansur Ibrahim ya aminta da karin lokacin da ‘yan sandan suka nema, kuma ya shigar da wata bukata ta neman bayar da belin wadanda ake tuhuma.
Jagoran lauyoyin ya karanto sashe na 157 da 161 (a'f) da sashe na 164 na dokar aikata manyan laifuka ta jihar Sokoto, da kuma sashe na 35(5) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 mai kwaskwarima a zaman hujjojin neman belin.
Kotun dai ta daga shari'ar zuwa wata rana da za a sanar da lauyoyin nan gaba, ta kuma bayar da umurnin a tura wadanda ake tuhumar gidan gyara hali.
Ku Duba Wannan Ma Daliba Ta Rasa Ranta A Sokoto Bayan Da Aka Zarge Ta Da Yin SaboWannan zaman kotun dai ya na zaman wani bangare na alkawali da gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi lokacin da ya gana da wakilan kungiyar Kirista ta kasa reshen jihar Sokoto a karkashin jagorancin Rev Fr. Nuhu Iliya, inda ya shaida musu cewa za a gudanar da bincike tare da gurfanar da duk wanda aka samu da laifi.
Har wa yau dangane da batun kisan Deborah Samuel, rundunar ‘yan sandan Najeriya, a wani bayani da ta fitar mai sa hannun kakakinta a Sokoto ASP Sanusi Abubakar, ta karyata wani bayani da aka wallafa a yanar gizo na cewa wata kwakkwarar majiya ta ‘yan sanda ta ce daya daga cikin wadanda ake tuhuma da kisan Deborah ba dan Najeriya ba ne, ya shigo ne daga Jamhuriyar Nijar a haramce ya aikata wannan aika-aikar.
Bayanin ya ce rundunar 'yan sanda ba ta fitar da kowane bayani mai kama da hakan ba, ta ce wasu ne da ke son tunzura jama'a da tayar da fitina suka kirkiri wannan labarin suka wallafa, inda ta bukaci jama'a da su rika yada batutuwan da za su kawo zaman lafiya a kasa.
Gwamnatin jihar Sokoto ta sassauta dokar ta baci da ta saka domin dakile tarzoma da matasa suka soma sanadiyar kama wadanda ake tuhuma a kisan Deborah.
Yanzu dokar ta kasance daga faduwar rana zuwa fitar ta.
Saurari rahoton Muhamad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5