An Kai Hare-hare Akan Kolejin Shi'a a Iraqi

  • Ibrahim Garba

Sojoji na duba inda aka kai hari.

An kai wasu jerin hare-hare da jefa bama-bamai akan kolejin 'yan shi'a a birnin Baghazada kasar Iraqi
A Iraqi, wasu jerin hare hare da aka kai, ciki har da wani farmaki da aka shirya kan wani koleji ‘yan shi’a dake birnin Bagadaza, ya kashe akalla mutane 14, ya jikkata wasu mutane su kusan hamsin, a jiya lahadi.

Wani dan harin kunar bakin wake tareda wasu ‘yan binidga sun auna hari kan jami’ar, inda suka kashe mutane biyar, suka raunana fiyeda mutane 13.

Jami’an kiwon lafiya sun tabbatar da adadin wadanda suka halaka da wadanda suka jikkata a harin, to amma babu wani bayani da aka samu a hukumance kan tarzomar.

Babu wanda ya dauki alhakin kai harin na boma bomai, amma tarzoma ta karu a duk fadin Iraqi saboda kudurin da yan yakin sa kai na kasar suka kudurta na yiwa gwamnatin kasar dake karkashin jagorancin ‘yan Shiya zagon kasa, gabannin zaben ‘yan majalisa da za ayi ranar 30 ga watan nan na Afrilu idan Allah ya kaimu.