Akalla mutum hudu suka mutu, bayan da wasu mahara suka far ma ofishin jadancin Faransa da cibiyar raya al'adun kasar da ke birnin Ouagadougou a Burkina Faso.
Shaidu sun fada ma kafar labarai ta AFP cewa wasu ‘yan bindiga 5 sun fito daga cikin wata mota su ka bude wuta kan wasu masu wuce wa kafin suka danna zuwa ofishin jakadancin.
Wani wakilin kafar labaran AFP ya ce ya ji ana mummunar musayar wuta, ya kuma ga wata mota na cin wuta, wadda aka ce ta ‘yan bindigar ce.
Wani kusar gwamnatin Burkina ya ce suna yi wa abin kallon kamar hari ne na ‘yan ta’adda.
A can Faransa kuma, shugaban kasar Emmanuel Macron, ya ce yana biye da abubuwan da ke gudana a babban birnin na Burkina Faso.
Wani sakon da aka saka a kafar sadarwa ta FaceBook ta ofishin Jakadancin Faransar na cewa, “ana shirin kai hari kan ofishin jakadancin Faransa da cibiyarta. Don haka kar a fito.”
Nan take dai babu wanda ya bugi kirji ya dauki alhakin wannan hari.