Hari da aka kai da gurneti kan wata motar safa a Nairobin kenya ya halaka mutane hudu
WASHINGTON, DC —
A Kenya an kai hari da wani makami da ake kyautata zaton gurneti ne kan wata motar safa a birnin Nairobi, har mutane hudu suka mutu.
Jiya Asabar ne aka kai harin yayinda motar take kan hanyar zuwa tsakiyar birnin daga unguwar da ake kira Easttleigh, inda galibin mazauna wurin ‘yan kasar Somalia ne.
‘Yansanda suka ce kimanin mutane 24 ne kuma suka jikkata a fashewar, kuma motar safan mai daukar mutane 32 ta lalace sosai, har da wasu motoci da suke kusa. Babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai wannan harin.
An kai harin ne kwana biyu bayanda wani mutum da ba san ko wanene bane ya jefa gurneti kan wata motar da take dauke da ‘yan kasar ingila biyu masu yawon bude ido a birnin Mombasa. ‘Yansanda suka ce gurneti bai tashi ba.
Har yanzu ana zaman dar dar sosai a Kenya tun bayanda mayakan sakai daga kungyar al-Shabab ta Somalia suka kai hari kan wata katafaren kasuwar zamani dake binrin Nairobi cikin watan satumba. Farar hula 61 da sojojin kasar shida ne suka halaka a harin.