Hare haren da sojojin na MNJTF suka kaddamar a dukkan iyakokin kasashen yankin, wato runduna ta biyu daga kasar Chadi da ake kira Sector 2, da runduna ta uku daga Najeriya wato Sector 3, da kuma runduna ta hudu wato Sector 4 daga sashen Nijer, an kai su ne a jere-a-jere lokaci guda, cikin tsari da yanayi na bai daya.
Zummar kai wadannan hare haren dai shine gamawa da 'yan ta'addan baki daya a yankunan na Tumbus da suka yi wa ka-ka-gida, inda kuma suke kitsa kai hare harensu.
Masanin harkokin tsaro, dakta Kabiru Adamu, ya ce a fahimtarsa, tabbas ire iren wadannan hare hare da dakarun MNJTF suke kaiwa kan sansanonin 'yan ta'addan, in har aka sami nasarar tarwatsa wadannan sansanonin aka kuma kama, ko kashe shugabannin mayakan, to babu shakka za a sami nasara wajen kawo karshen 'yan ta'addan.
"Akan sami nasara a yaki ta hanyoyin da ake kira Attrition da Deception da turanci, wato jajircewa wajen takura abokan gaba da zafafan hare hare har sai sun ji ba sarki sai Allah. Bayan haka kuma a yi ta auna manyan jagorori da kwamandojin mayakan kamar yadda rundunar MNJTF keyi a yanzu, a cewar masanin tsaro dake zama tsohon babban Hafsa a rundunar sojin Najeriya, Wing Commander Musa Isa Salmanu.
Wing Commander Salmanu ya kuma ce ya gamsu da yadda rundunonin dake karkashin babbar rundunar kasashen tafkin Chadi ke aiki kafada da
kafada cikin tsari, wanda hakan na kara basu nasara sosai a fafatawar
da suke yi a halin yanzu.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5