Wasu 'yan bindiga dake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai farmaki a kan makarantar sakandaren mata ta garin dapchi dake Jihar Yobe.
An kai wannan hari da maraicen jiya litinin.
Wani malamin makarantar, wanda ya samu kubuta, yace shi da wasu dalibai sun samu nasarar tserewa zuwa cikin daji, yayin da wasu suka samu sukunin sulalewa zuwa cikin gari.
Kwamishinan 'yan sandan Jihar Yobe, Mr. Abdulmalik Saminu, ya tabbatar da abkuwar wannan lamarin inda yake cewa wasu mahara ne suka far ma makarantar.
Malamin makarantar da ya ga wannan abu da idonsa, yace an kawo musu farmakin ne da misalin karfe 7, daidai lokacin da suke tsakiyar sallar magariba, inda suka yi ta jin harbe-harbe.
Babu wani bayani a kan ko an sace wasu daga cikin daliban makarantar ko an ji rauni ma wasu a harin har zuwa wannan lokacin.
Malamin da ya bayar da shaidar ya fadawa wakilinmu Haruna Dauda cewa "sun shiga makarantar har bakin kofar gidana, ban san yadda nayi ma na fita ba.
"Ban san inda iyali na suke yanzu ba. Ba zan iya ba da rahoton ko an dibi dalibai ko ba a diba ba, amma yaran wasu mun shigar da su cikin gari, wasu mu na tare da su yanzu haka a daji. Iyali na dai ban san ta inda suka bi ba."
Malamin yana cewa, "wadanda suka shiga wurinmu da motoci suka zo, samfurin Tata mai fentin sojoji. Na ga motoci uku, daya a kofar gidana, daya a gefen masallaci, daya kuma ta gefen dakin kwanan dalibai."
Shaidar ya ci gaba da cewa a bayan makarantar sakandaren ta mata sun shiga cikin gari. Yace a yayin da suke cikin dajin sun samu labarin cewa sojoji sun shigo cikin garin na Dapchi.
Har yanzu babu wani bayani na irin barnar da aka aikata a lokacin wannan harin a garin Dapchi, dake karamar hukumar Bursari, mai tazarar kilomita dari da wani abu a arewa da Damaturu a kan hanyar zuwa Gashua.
Your browser doesn’t support HTML5