An Kafa Wata Sabuwar Kungiya Ta Farfado da Martabar Arewacin Najeriya

Yayin da mazauna lardin arewacin Najeriya ke fama da kalubalen tsaro da tattalin arziki da kuma rashin ayyukan yi, an kafa wata sabuwar kungiya da nufin farfado da martabar yankin na Arewa.

Dimbin albarkatun karkashin kasa, da na al’umma, da arzikin kasar noma da kuma zaman lafiya na daga cikin abubuwan da yankin arewa ke alfahari dasu.

Sai dai a shekarun baya-bayan nan wadannan abubuwa sun kama tafarkin gushewa, lamarin da ya sanya aka kirkiro da wata sabuwar kungiya mai suna “Northern Reform Organization” ko NRO a takaice.

Alhaji Faruk Usman, shi ne sakataren labarai na kungiyar, ya ce an kirkiro kungiyar ne saboda a yi kokarin farfado da mutunci, ayyuka, da bukace-bukace na al’ummar arewacin Najeriya.

Yanzu haka dai wannan sabuwar kungiyya ta NRO ta fayyace wasu al’amuran raya arewa da ta ce ya kamata gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su maida hankali akan su.

Dr. Dalhatu Sani Yola, memba ne a kwamitin amintattu na kungiyar, ya ce suna danganta matsalar tsaro da ake fama da ita da rashin aikin yi, rashin masana’antu, da koma bayan tattalin arziki a yankunan na arewacin Najeriya.

Ya kara da cewa, abinda kungiyar ta sa a gaba shi ne ganin an samar da wadannan abubuwan na raya kasa, da ankarar da gwamnatoci da masu ruwa da tsaki abubuwan da arewacin kasar ke bukata, tare da hada hannu da kungiyoyin ciyar da arewa gaba kamar ACF ta dattawan arewa, wadda ke daga cikin muradun sabuwar kungiyar ta NRO.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

Your browser doesn’t support HTML5

An Kafa Wata Sabuwar Kungiya Ta Farfado da Martabar Arewacin Najeriya