A yanzu haka akwai matsalolin rashin tsaro kama daga ‘yan bindiga da suka addabi yankunan Arewa maso yamma da kuma Arewa maso tsakiyar kasar, yayin da a yankin Arewa maso gabashi kuma ake fama da matsalar ‘yan kungiyar Boko Haram, wadannan duk sun taka rawa a kalubalen da ake fuskanta ta fannin ilimi.
Wadannan Matsaloli da suka yi dabaibayi tare da kawo wa sashen ilimin cikas ya sa a yanzu haka wasu sarakuna iyayen kasa suka fara daukar matakin kafa wasu kwamitoci na musamman don farfado da sashen ilimi da bunkasa tattalin arziki a yankunansu.
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Neja Amb. Ahmed Musa Ibeto Santurakin Kontagora, shi ne shugaban kwamitin amintattu na wasu manyan kwamitocin bunkasa ilimi da tattalin arziki a masarautar Kontagora da ke jjhar Neja, yace an bar arewa a baya a fannin ilimi, shi ya sa aka kafa kwamitin.
Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Neja Dr. Muhammad Makusidi, ya ce matakin da masarautar Kontagora ta dauka abin koyi ne ga sauran masarautun yankin Arewacin Najeriya.
Mai Martaba Sarkin Sudan na Kontagora Alhaji Muhammadu Barau Mu’azu na biyu, ya ce sun dauki wannan mataki ne don kokarin cike gurbi ko ratar da aka ba yankin Arewacin Najeriya ta fuskar ilimi, a saboda haka yayi fatan ‘yan kwamitin zasu bai wa marada kunya.
Saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari:
Your browser doesn’t support HTML5