An Kafa Kwamitin Dakile Shishshigin Rasha a Zabukan Yamma

  • Ibrahim Garba

Robert Mueller, mai binciken tsakalandan din Rasha a zaben Amurka.

A yinkurinsu na maganin gaba, wasu masu ruwa da tsaki sun dau matakin ganin Rasha da sauran kasashe masu salo irin nata ba su yi shishshigi a zaben kasashen yammacin duniya ba.

An kafa wani kwamiti na kasa da kasa da zummar kawo karshen shiga sharo ba shanun da kasar Rasha da sauran kasashe masu bin tafarkin murdiya ke yi, a tsarin dimokaradiyyar yammacin duniya.

Kwamitin mai suna Transatlantic Commission on Election Integrity, ko Hukumar Tabbatar Da Ingancin Zabe Na Yankin Atlantic da ma gaba (TCEI) a takaice, da ke karkashin jagorancin hadin gwiwar tsohon Sakatare-Janar din NATO Anders Fogh Rasmussen da kuma tsohon Skataren hukumar tsaron gida ta Amurka Michael Chertoff, ya kira taron manema labarai ranar Jumma’a a birnin Washington DC.

Musabbabin kafa kwamitin shi ne “katsalandan din da Rasha ta yi a zaben Amurka na 2016,” a cewar Rasmussen ga Sashin Rashanci na Muryar Amurka. Ya kara da cewa, “To amma ba kawai game da Amurka ba ne. Har ma da bangaren Turai. Mu a Turai mun fuskanci kalubale, kuma wannan ne ma dalilin da ya za hurumin kwamitin ya zarce yankin Atlantika.” Ya ce akwai zabuka wajen sama da 20 da ke tafe a yammacin duniya gabanin zaben Shugaban kasar Amurka na 2020.