Ma’aikatar Shari’a a jihar Bauchi, ta bullo da wani tsari ta hanyar kirkiro da kananan kotuna da za su rika bin hakkokin mutane musamman bashin kudade da ake bin su da ba su haura naira miliyan uku ba.
Kotun za ta tabbatar ta kammala sauraren karar da aka shigar gabanta cikin kwanaki sittin.
Mai Shara’a Mu’azu Abubakar a tattaunawa da shi kan wannan sabon tsarin samar da kananan kotunan ya ce, makasudin kafa kotunan shi ne saukakawa wajen isa ga kotuna domin neman hakki kan lokaci.
“Babban makasudin kafa wannan kotun shi ne saboda a saukaka wa mutane isa kotuna don gabatar da damuwar da ya dame su, ya zamanto kuma an saukaka irin magudi da ba ta lokaci da ake samu.” in ji Alkalin babban kotu, Mu’azu Abubakar.
Kan wannan hobbasar da ma’aikatar Shari’a ta jihar Bauchi ta bijiro da shi ta hanyar kafa kananan kotunan domin karban kudaden daga hannun mutanen da ake binsu bashi, wasu daga cikin al'umar jihar Bauchi sun yaba da tsarin.
"Wannan abin murna ne da farin ciki ga duka bangarori guda biyu, mu kan mu ‘yan kasuwa ha’inai daga cikin mutane wanda su karbi kayan mutane ko kamfanoni su hana kudin su ki biya wannan kotu zata taimaka kwarai da gaske.” A cewar dan kasauwa Ibrahim Arab.
Har ila an ji ta ta bakin shugabannin addinai kan samar da kotunan da jihar Bauchi ta yi.
“Muna godiya ga Allahu Subhanahu wata’ala da ya baiwa Judishiari ta Jihar Bauchi dama ta fuskar ainihin addini” in ji Imam Sa’id Dalhatu Bawa limamin massalacin juma’a na kan titin Murtala Muhhamad
Saurari cikakken rahoto cikin sauti daga Abdulwahab Muhammad.
Your browser doesn’t support HTML5