Wannan sabuwar hukumar zata yi aiki ne da ma’aikatun kan iyakokin da daman ake da su a cikin kasashen 28 dake cikin K-T-T din, inda zasu hada kai su rinka bankado duk wata barazana ga harakokin tsaron kasashen.
Haka kuma sabuwar hukumar, wacce zata fara aiki a watan Maris na 2017, zata taimaka wajen ganin an sawwaka musayar bayanai a tsakanin ma’aikatin tsaro da na leken assirai na kasashen da abin ya shafa, a cewar Fabrice Leggeri, Darektan Hukumar Kan Iyakokin na Turai.
Rahottani sunce kafa Hukumar yana faruwa ne a sanadin dimbin yawan ‘yan gudun hijiran da suka rinka kwarara a cikin kasashen Turan a ‘yan shekarun nan, wanda akace ba’a ga mai yawansu ba tun karshen Yakin Duniya na Biyu.
A shekarar da ta gabata kadai, kasashen Turai sun karbi bakuncin bakin haure sun kai milyan 1 da dubu 500.