Wannan dai ya faru ne bayan kisan gillar da wasu 'yan bindiga su ka yiwa wasu ‘yan banga guda 4 a wani kauyen tashar kare dake kusa da Kagaran,
Al’amarin da ya tunzura mutanen yankin suka afkawa Ofishin ‘Yan Sandan tare da kwashe bindigogi sama da guda 10.
A cikin hirarshi da Muryar Amurka, shugaban karamar hukumar Rafin, Alhaji Isma’ila Modibbo ya ce kusan kwana biyar kenan a Karamar Hukumar Rafi ake samun hare hare na ‘yan bindiga wanda ya tunzura mutanen gari suka kaiwa ‘yan sanda farmaki har suka lalata kadarori kuma suka kwace bindigogi kusa ngoma sha daya. Ya kuma bayyana cewa, an kafa dokar hana fitan ne da nufin ganin an sami kwanciyar hankali.
A nashi bayanin, kwamshinan ‘Yan Sandan jihar Nejan, Alhaji Adamu Usman, yace suna bincike akan lamari,
Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5