An Kafa Dokar Hana Hawa Babura Daga Karfe 6 Na Yamma A Birnin Minna

NEJA: GWMNAN JIHAR NEJA Alhaji Abubakar Sani Bello

A fadar gwamnatin jihar Neja, Minna, an kafa dokar ta hana hawa babur daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 6 na safiya.

Gwamnatin dai tace ta dauki wannan mataki ne domin ‘kara tsaurara tsaro a birnin Minna, biyo bayan harbe wasu jami’an ‘yan sanda biyu har lahira da wasu ‘yan bindiga suka yi ranar Lahadi.

Kwamishinan labarai na jihar Mr. Jonathan Batsa, ya tabbatar da cewa an kashe ‘yan sanda biyu an kuma ‘dauke musu bindigoginsu, ya kuma ce dalilin kafa wannan doka itace domin mutanen da suka aikata wannan laifi sunzo ne kan babura.

Rundunar ‘yan sandan jihar tace tana nan tana farautar mutanen da suka kashe ‘yan sandan, a cewar kakakin rundunar DSP Bala ElKana.

Wannan dai na zuwa ne ‘kasa da mako guda da kisan wasu sojoji 11 da kuma fararen hula 7 a kauyen Kopa dake karamar hukumar Bosso.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kafa Dokar Hana Hawa Babura Daga 6 Na Yamma A Birnin Minna - 2'55"