Asusun da kwamitin Janaral T.Y. Danjuma, tsohon hafsan hafsoshin sojojin Najeriya, zai jagoranta zai tallafawa wadanda rikicin ya shafa. Asusun zai sake tsugunar da mutane da inganta rayuwa da kuma dawowa da martabar ilimi da cinikayya da sauran abubuwa na more rayuwar wadanda tashe-tashen hankulan ya wargaza a wannan yankin na arewa maso gabas.
Bayan da aka kaddamar da kwamitin ne ministan watsa labarai na Najeriya Labaran Maku ya yiwa manema labarai karin bayani akan ayyukan kwamitin din. Kamar yadda shugaban kasa ya fada a tuna da 'yan kasar dake yankin arewa maso gabas. A kaunaci juna a yi taimako. Yakamata a tashi a san yadda za'a yi a taimakesu.
Minitan yace ba za'a san yawan mutanen da abun ya shafa ba sai lokacin da kwamitin ya fara zagayawa kana a san yawan adadin wadanda lamarin ya shafa. Kodayake an kafa kwamitin din, ministan yace bai san ko nawa gwamnati zata saka cikin asusun ba.
An tambayi Labaran Maku idan wasu da lamarin bai shafesu ba amma suka fito suka ce ya shafesu shin yaya gwamnati zata tantancesu ko kuma wadanne irin matakai za'a iya dauka domin kada wadanda basu cancanta ba su shiga cikin tallafin. Ministan yace suna fata wadanda abun bai shafesu ba zasu gujewa yin karya ganin irin fitinar da kasar ta shiga. Amma ya kira mutane da su ji tsoron Allah. Shugaban kwamitin Janaral Danjuma ya bada tabbacin za'a yi aikin cikin gaskiya da adalci.
Kawo yanzu dai alkalumma sun nuna mutane sama da miliyan uku suka rasa matsuguninsu a yankin arewa maso gabas.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.
Your browser doesn’t support HTML5