A ranar 21 ga watan Fabrairu mai kamawa ake sa ran za a yi zaben shugaban kasa a zagaye na farko, inda tuni hukumar zabe ta CENI ta ce ta fara raba katunan zabe a sassan kasar, kamar yadda shugaban hukumar, Boube Ibrahim ya tabbatarwa Sashen Hausa na Muryar Amurka.
A daya bangaren ‘yan adawa sun yi ikrarin cewa shugaban kasar Issoufou Muhammadou ya fara yakin neman zaben tun lokaci bai yi ba, zargin da gwamnatinsa ta musanta.
Wani batu kuma da ya kunno kai a karshen makon da ya gabata shi ne zargin gwamnatin kasar na yin amfani da wasu sakarunan gargajiya wajen yakin neman zabe, zargin da shima gwamnatin ta musanta.
'Yan takarar shugaban kasa 15 ne za su fafata a wannan zabe ciki har da shugaba mai ci Issoufou Muhammadou.
Domin jin cikakken bayani kan yadda aka fara yakin neman zaben, saurari wannan rahoto na wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barmah.
Your browser doesn’t support HTML5