An Kaddamar Da Wasu Sabbin Sauye Sauye A Hukumar Gidajen Gyara Hali Ta Najeriya

Gidan gyara hali

Hukumar gidajen gyara hali ta Najeriya ta kaddamar da wasu sauye sauye da a cewarta za su inganta ayyukan ma’aikatanta da rayuwar fursunoni da ake tsare da su a fadin kasar.

Hakan dai ya biyo bayan rattaba hannu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kan dokar da ta bada damar tabbatar da umarnin canja sunan hukumar a shekarar 2019 daga yadda aka santa a baya watau gidajen kurkuku zuwa gidajen gyara hali.

Ministan harkokin cikin gida a Najeriya, Rauf Aregbesola ya kaddamar da ayyukan a hedikwatar hukumar dake Abuja wadanda suka hada da bude wani sashin fasahar sadarwa ta zamani da zai sa ido kan harkokin da ke gudana a hukumar tare da ba rahoto akai akai wanda a yanzu haka aka samar a Abuja kafin daga bisani a bude a wasu jihohin da ke kasar da kuma motoci iri daban daban na aiki, kazalika an sauya kayan sarki watau tufafin aiki da jami’ai a hukumar ke sanyawa zuwa wasu sabbi na daban.

Gidan gyara hali

Maryam Adamu wacce ke matsayin Kwanturola a hukumar ta bayyana cewa wannan canji da aka samar zai taimaka wajen daga daraja da kimar hukumar daga yadda ake mata kallo a baya can.

Shugaban hukumar ta kasa Haliru Nababa ya bayyana cewa canja sunan hukumar da doka ta ba dama a yi zai taimaka wajen gyara halin fursunonin da ake tsare da su wajen samar musu rayuwa mai kyau haka kuma hukumar ta fitar da wani tsari da zai na zakulo hazikan jami’ai a hukumar wadanda suka yi rawar gani a yayin gudanar da ayyukansu tare da ba su lambar yabo da nufin karfafa musu gwiwa.

Tsohon shugaban hukumar ta gidajen gyara hali a Najeriya Jafaru Ahmad wanda a karkashin shugabancinsa aka fara wannan aiki na samar da sauye sauyen ya bayyana cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an inganta rayuwar duk wani fursuna da aka kawo gidan gyara hali a kasar.

A na dai hasashen wannan cigaba da hukumar ta samu za su taimaka wajen rage hare hare da ake yawan kaiwa gidajen gyara hali da ake da su a fadin Najeriya.

Saurari rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

An kaddamar da wasu sabbin Sauye Sauye A Hukumar Gidajen Gyara Hali Ta Najeriya.mp3