Hukumar hana fataucin mata da yara ta Najeriya da ake kira NAPTIP a takaice, ta fito da wani kundi wanda za a dinga rijistar masu aikata laifin fyade da wasu laifukan makamanta wannan.
Kundin rijistar dai zai zama wani muhalli da za a shigar da sunayen wadanda a ka samu da wannan laifi don ko da ba a yi mu su wani hukunci mai tsanani ba a karkashin dokokin Najeriya, jama’a zasu iya sanin su don yin taka-tsan-tsan da su, a cewar Julie Okah Donli, shugabar hukumar ta NAPTIP.
Babban mai shigar da kara na Najeriya, Dayo Apata da ya halarci taron kaddamar da kundin rijistar a madadin mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce akwai matakan da kowannen mu zai iya dauka wajen kawar da duk wani nau’in cin zarafin mata da suka hada da daina muzanta su ko dora laifi akan wadanda aka ci zarafin su, da koyawa yara maza kare mazantakar su ta hanyar mutunta mata, da kuma muhimmancin sanar da ‘yan sanda ko jami’an yaki da cin zarafin mata idan an ga wani abu mai kama da haka iya faru.
Aisha Zakari Yasmin, da ke sharhi akan lamuran mata da yara ta yi marhabin da wannan kundin ta kuma bukaci a yi tsayin-daka akan muradin.
Wani matashi a arewacin Najeriya mai suna Anas Dan Na-yaba, shi ma ya yaba da wannan matakin ya kuma ce kamata yayi duk wanda aka samu da laifin fyade a yanke mashi hukuncin kisa.
Laifin fyade dai ya kusan zama ruwan dare a Najeriya abinda ya sa jama’a ke yin kiran a yi dokoki masu tsanani don hukuncin gani ga wane.
Ga karin bayani cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5