Ma’aikatar Ayyukan Mata a Najeriya ta kaddamar da shirin tara bayanai akan batutuwan cin zarrafin mata da yara da cin zarafi da suka shafi na jinsi.
Ma’aikatar Ayyukan Matan a karkashin jagorancin Minista Pauline Tallen ta kaddamar da shiri da ya kunshi dandali da kundin tara bayanai akan cin zarrafin mata da yara da cin zarrafi da suka shafi na jinsi din ne ta hayar yin amfani da fasahar zamani domin kawo karshen matsalolin da suka addabi al’umma.
Dandalin tattara bayanai akan batutuwan cin zarrafin mata da yara, ingantaccen dandali ne na sarrafa bayanai da tsarin dake amfani da fasahar zamani domin bai wa gwamnati, masu ruwa da tsaki, da kuma masu sa ido a kan batutuwan da suka shafi cin zarafi damar yin nazari a kan bayanan da za a rinka tattarawa a sauwake kamar yadda Minista Tallen ta bayyana. Minista Tallen, ta yi jan hankali a kan shirin tattara bayanan.
A jawabin ta a lokacin taron, Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina Muhammad ta ce, za a yi amfani da damar yanayin da duniya ke ciki na annobar korona wajen magance matsalolin da suka shafi na jinsi a cikin al’umman mu cikin gaggawa.
A cikin makon da ya gabata ne asusun kula da yawan jama’a na majalisar dinkin duniya wato UNFPA, ya shirya taron horas da ‘yan jaridu a kan inganta yadda su ke hada rahoton da suka shafi matsalolin cin zarrafi na jinsi inda Hajiya Kori Habib, masaniya a kan sha’anin yada labarai na asusun, ta yi karin bayani.
Bisa ga kididdigar nazarin lafiya a Najeriya na shekarar 2018, kaso 31 na mata masu shekaru daga 15- 49 sun fuskanci matsalar cin zarrafi akalla sau daya a rayuwarsu, kuma kaso 13.7 cikin matan da aka yi nazari tare da su sun fuskanci cin zarrafi a zahiri cikin watanni 12 da suka gabata.
A fadin duniya, kaso 30 cikin 100 na mata sun fuskanci cin zarrafi kuma an samu adadi mafi yawa a nahiyar Afrika, gabashin Bahar Rum, da kudu maso gabashin Asiya da kaso 37 cikin 100.
Ga Halima Abdulra’uf da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5